Babban kalubalen da muke fuskanta a matsayinmu na masu shirya fina-finai ga gidajen talabiji shine rashin sayen fina-finanmu da muhimmanci inji shugaban kungiyar masu shirya fina-finai don gidajen talabiji ko satellite TV Sani Sule Katsina, wanda aka fi sani da garkuwan matasa.
Ya ce tashoshin talabijin kamar tashar Arewa 24, na kawo wa harkar cikas ta hanyar wulakanta musu fina-finansu wajen saye a kudi kalilan, ya ce tun suna saye da kudin Amurka, wato da dala har ta kai a yanzu sun sauko da farashin kasa inda suke biya da naira.
Garkuwar matasa ya ce a yanzu ma ya kai matsayin da sun sauko da farashin fim din kasa inda suke saye a matsayin fim daya, kudinsa baya dara naira dubu dari, maimakon naira dubu dari takwas da wasu tashoshin ke saye.
Ya ce a iya saninsa ya kalubalanci tashar Arewa 24, da ma sauran tashoshin da suke yin haka ta hanya sai su sayi fim din su sannan suki biya akan lokaci kuma a wulakance bayan sun gama sanya fim din a tashoshinsu.
Malam Sani ya ce don hake ne ya sa suka kafa kungiyar content producer wato kungiya mai lura da masu shirya fina-fina don gidajen talabijin da satellite Tv.
Facebook Forum