Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fararen Hula Da Suka Gudu Daga Garin Malakal Sun Koma Gidajensu


Dubban dubatan fararen hula da suka gudu daga garin Malakal na Sudan ta Kudu lokacin yakin da ya barke a shekarar 2013 sun koma gidajensu.

Har yanzu, garin na fama da jimamin abin da ya faru a Sudan ta Kudu shekaru biyar da suka gabata. Har yanzu akwai ramukan harsashai a bangon gine-ginen da basu rushe ba. Mutane sun fara kasuwanci a cikin rugurguzazzun shaguna.

Baya ga kokarin sake gina garin, mazauna yankin suna kokarin sake gina gidajensu da kuma gano mutanen da suka bace a lokacin yakin. Kwamitin harkokin wajen kasa na Red Cross yana taimaka musu da binciko wandanda suka bata.

Dangi dake kokarin neman sanin labaran 'yan uwansu da suka bace, sukan tsaya a layi a wuraren dauke da hotuna ‘yan uwan nasu a cibiyoyin kwamitin agaji na Red Cross wato ICRC a takaice.

A bara, kwamitin agaji na Red Cross ta Sudan ta Kudu, ya sake hada mutane 68 da suka rabu da iyalansu a lokacin rikici.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG