Faransa da ke rike da kofin duniya, ta kwato kanta da kyar a hannun Ukraine a ci gaba da wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da ake yi.
An tashi a wasan ne da ci 1-1.
Ukraine ce ta fara zura kwallo a ragar Faransa ta hannun dan wasanta Mykola Shaparenkoto a minti na 44 - gab da ana shirin zuwa hutun rabin lokaci.
Minti biyar bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Anthony Martial ya farkewa Faransa kwallonta.
Wannan shi ne karon farko da Martial yake ci wa Faransa kwallo a wasannin da yake buga mata tun bayan 2016.
A wannan rukuni na D, wasanni bakwai da aka buga cikin 10 duk an tashi ne da kunnen doki, inda biyar daga cikinsu suka shafi Ukraine.
Faransa ce ke saman teburin da maki tara a wasanni biyar da ta buga amma Finland wacce ke matsayi na biyu da maki biyar na da wasanni biyu da za ta buga a nan gaba.
A wasu daga cikin wasannin da aka yi, Ireland ita ma ta tashi da ci 1-1 da Azerbaijan, Scotland ta doke Maldova da ci 1-0.
Netherland ta lallasa Montenegro da ci 4-0 yayin da Finland ta doke Kazakhstan da ci daya mai ban haushi.