Shugabannin kasashen G5 Sahel da na Faransa sun jaddada aniyar ci gaba da aiki kafada da kafada a yakin da suke gwabzawa da ‘yan ta’adda.
Yayin taron wadan suka kammala a garin Pau da ke kasar Faransa, shugabannin sun bayyana shirin bullo da wasu sabbin matakai kan yadda za su tunkari matsalolin tsaro a yankunansu.
Sai dai masu adawa da zaman sojojin Faransa a wannan yanki, sun ce za su ci gaba da nuna matsin lamba har sai rundunar samar da tsaro a yankin da ake kira "Barkhane" ta kwashe komatsanta.
Taron wanda aka bayyana a matsayin na sake daura damarar yaki da ta’addanci a Yankin Sahel, ya yanke shawarar ci gaba da zaman sojan Faransa a wannan Yanki,.
Wannan dalili ya sa Faransa ta amince ta aika karin sojoji 220 akan 4,500 da ke can tun farko, matakin da dan Majalisar Dokokin Kasa, Idrissa Maidaji ya ce ya yi daidai.
Haka kuma an bayyana shirin hada gwiwa tsakanin dakarun rundunar ta Barkhane da na G5 Sahel domin aiki a karkashin jagorancin kwamanda 1.
Sai dai shugaban kungiyar AEC Moussa Tchangari na ganin yin hakan, tamkar sakarwa Faransa ragamar komai na sha’anin tsaro a kasashen Sahel ne.
Tun ba yau ba dai talakawa a kasashen Sahel ke zargin Faransa da yunkurin shimfida sabon salon mulkin mallaka ta hanyar kafa sansanin soja a wannan yanki, abin da shugaban jam’iyar PND Awaiwaya Soumaila Amadou, ya ce shi ne ya fara bayyana a fili a karshen taron na Pau.
Musayar bayanai, da gudanar da ayyukan samar da walwalar jama’a, na daga cikin abubuwan da shugabannin G5 Sahel suka ce za su maida hankali akansu a wani bangare na yaki da ta’addanci.
Anan gaba kadan ne za a soma zartar da shawarwarin da taron na birnin Pau ya tsayar.
Sannan kasashen Mali, Burkina Faso, Chad, Nijar, Mauritania da Faransa sun dauki alkawarin haduwa lokaci zuwa lokaci domin bitar halin da ake ciki a wannan yaki da ke kokarin gagarar kundila.
Saurari cikakken rahoto cikin sauti daga Nijar:
Facebook Forum