Jam’iyyar shugaban Falasdinu Mahmud Abbas ta yi kira da ayi zazzafar zanga-zanga lokacin ziyarar mataimakin shugaban Amurka Mike Pence zuwa birnin Kudus mako mai zuwa.
A jiya Asabar ne jam’iyyar Fatah ta sanar da cewa “Muna kira da a gudanar da zanga-zangar nuna fushi a kofar shiga birnin Kudus da kuma tsohon birnin ta a daidai lokacin ziyarar da mataimakin shugaban Amurka zai kawo ranar Laraba, domin nuna rashin amincewa da shawarar da Trump ya yanke kan birnin Kudus.”
Farkon watan nan ne Trump ya fusata Falasdinawa lokacin da ya sanar da cewa Amurka ta amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, wanda hakan ya zama warware daidaituwar da aka cimma mai sarkakiya tun shekaru masu yawa. shugabannin Falasdinu sun mayar da martani ta hanyar soke ganawar da aka shirya zasu yi da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence. Har yanzu dai ana sa ran zai gana da jami’an Isra’ila.
Baki ‘daya dai Falasdinawa da Isra’ilawa na ‘daukar birnin Kudus a matsayin babban birnin su na gaskiya. Amma jayayyar da ake kan birnin yasa ake gudanar da harkokin gwamnati a wasu wurare, inda birnin Tel Aviv ya zamanto na Isra’ila sai kuma Ramallah na hukumomin Falasdinawa.
Sanarwar da Trump yayi dai ta harzuka Falasdinawa, ta kuma haifar da zanga-zanga daga dubban Falasdinawa a gabas ta tsakiya da sauran yankuna.
Facebook Forum