Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Tarayyar Turai Ta Gaza Cimma Matsaya


High Representative for Foreign and Security Policy of the European Union Federica Mogherini and Minister of Foreign Affairs of Croatia Marija Pejčinović Burić.
High Representative for Foreign and Security Policy of the European Union Federica Mogherini and Minister of Foreign Affairs of Croatia Marija Pejčinović Burić.

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun gaza cimma matsaya akan batu bakin haure.Hakan ko ya biyo bayan taron da kungiyar tayi ne Brussel.

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai sun kammala taron su a Brussel kuma sun amince cewa Birtaniya tayi dukkan abinda ya dace, don haka tana iya shiga rukuni na biyu na ficewa daga kungiyar, sai dai ba wata alamar tattaunawar da suka yi game da batun shige da fice.

Shugaban majilisar kungiyar Donald Tusk, yasa batun shige da fice a cikin babban agenda a taron nasu na kwanaki biyu.

Yace a karshen taron nasu jiya jumaa, shugabannin kungiyar zaiyi wahala ace sun cimma matsaya akan sabon tsarin karban bakin hauure, musammam a zuwa karshen watan watan yuni.

Tusk ya shaidawa taron manema labarai jim kadan da kammala taron cewa babban matsalar ko ita ce adadi mafi karanci da kowace kasa zata karba, duk da yake adadin ya ragiu amma fa cimma matsaya abu ne mai wahala.

Jamiaan kungiyar sun kwashe sama sa sao’I biyu suna tafka mahawara mai zafin gaske akan wannan batu na shige da fice a tsakanin su, amma sun gaza cimma matsaya domin ko an ta samun raayoyi mabanbanta, kamar yadda Prime Ministan Holland Mark Rutte yake cewa bayan kammala taron.

Daga karshe dai Tusk wanda shima tsohon Prime Minista ne yace ma shugabannin kungiyar yayi a jingine maganar amma a tabbatar an cimma matsaya a cikin watan yunin shekara mai kamawa.

Wannan batun dai na shige da fice musammam na bakin haure shine kadai wanda kungiyar ta gaza cimma matsaya akan sa, bako sabo da kome bane sai domin adadin da kowace kasa zata dauka ko amince dashi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG