Sakamakon taron ya nuna an samu nasarori masu dimbin yawa dangane da shirye shirye da daura damarar da aka yi na tabbatar da an tallafawa kasashe masu tasowa. Suma manyan kasashe wadanda sune keda alhakin dumamar yanayi, sunce zasu matakai da dabaru na magance wannan matsalar ta dumamar yanayi..
Taron ya kuma yi nazarin hanyar kawar da barkewar babbar annoba a duniya baki daya wanda zata iya yin sanadiyar gurbata yanayi da zai kawo karancin abinci da kuma walwala na al’ummar duniya. Kasar Amurka dai, itace kasa daya a duniya da ta janye daga yarjejeniyar da aka kula domin taimakawa bil adama daga dumamar yanayi.
Ministan kula da muhalli na Najeriya Ibrahim Usman Jibrin yace da farko ana zaton za a samu cikas saboda janyewar Amurka daga yarjejeniyar yanayi ta Paris, amma kuma shugabanin duniya da suka halarci wannan taro suna ganin ficewar ta ba zai rage tasirin yarjejeniyar ba.
Facebook Forum