Wata babar kotu a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria ta sauke mukadashin shugaban jam'iyar PDP na kas Uche Seondus daga kan mukamin sa. Kotu ta yanke hukuncin ne akan cewa Mr Secondus yana kan mukamin ne ba bisa ka'ida ba.
Tsohon mai baiwa shugaban Nigeria shawara Ahmed Ali Gulak ne ya shigar da karar. Yace ya kai kara kotu ne domin a gyara jam'iyar PDP, domin yace a lokacinda shugaban PDP na kasa Alhaji Ahmed Adamu Muazu yayi murabus, ya kamata daya daga cikin 'yan jam'iyar daga arewa maso gabashin Nigeria su maye gurbin sa.
To amma mukadashin shugaban jam'iyar Uche Scondus yayi babakere, yace sam ba zai sauka ba.
Alhaji Gulah yace Mr Secondus ya yi kusan watani bakwai akan wannan mukami, amma ba shi da niyar yin abinda ya kamata, yace shi yasa suka garzaya zuwa kotu.
Kotu dai ta baiwa Mr Secondus wa'adin makoni byu daya tattara enasa enasa ya bar kujerar shugaban PDP na kasa.