Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu da ta arewa suna tattauanawa duk da tankiyar dake tsakaninsu


Shugabannin Kungiyar Tarayyar Kasashen nahiyar Afrika
Shugabannin Kungiyar Tarayyar Kasashen nahiyar Afrika

Ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu

Ana ci gaba da tattaunawa a tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu a yayin da suke kokarin warware sabani mummuna da suke yi kan man fetur da bakin iyaka da kuma zamowa dan kasa.

Wani wakilin Muryar Amurka a zauren taron da ake yi a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia, yace tattaunawar tana mayarda hankali a kan batutuwan iyaka, yayin da masu shiga tsakani na Kungiyar Tarayyar Kasashen Afurka suke kokarin samo inda sassan biyu zasu iya daidaitawa a game da batutuwa masu sosa zuciya na raba arzikin man fetur da kasancewa dan kasa.

Sudan ta Kudu tana zargin Sudan da laifin cajin kudin da ya wuce misali na yin amfani da bututun mai da ya bi ta arewa zuwa bakin gabar Bahar Maliya. Wata majiya a kusa da zauren taron ta fadawa Muryar Amurka cewa Sudan ta Kudu tana tayin biyan kimanin Naira 110 a kan kowace gangar mai daya da ta bi ta bututun, amma Sudan tana son a rika biyanta har Naira Dubu 5 da 750 a kan kowace gangar mai daya da ta bi ta cikin wannan bututu.

Sassan biyu sun gana a daren jiya laraba domin nazarin ko ya dace su ci gaba da shawarwarin da aka shirya na kwanaki 10, amma kuma ya rikice ya koma zage-zage da ihu a ranar talata.

XS
SM
MD
LG