Wani tsohon ma’aikacin wucin gadi a kanfanin Facebook a jihar California, ya garzaya kotu inda ya zargi kantafaren kanfanin da rashin bada kulawar data dace ga ma’aikatan kanfanin dake kula da tantance al’amuran da suka shafi munanan hotuna ko bidiyo dake fama da damuwa.
Kotun ta bayyana cewa ‘yan kwantaragi dake kula da wannan bangare na kanfanin Facebook, na fama da munanan hotuna da bidiyo dake nuna yadda ake cin zarafin kananan yara, da fyade da fillar kawuna da kunar bakin wake da sauran munanan ayyuka makamantan su.
Kanfanin Facebook ya yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa na samar da wurin aiki ga ‘yan kwangila kamar yadda ya dace amma sai aka wayi gari lamarin ya zama wasan yara a cewar Korey Nelson, lauyan tsohon ma’aikacin dan kwagila a kanfanin Facebook cikin wani jawabin da ya fitar a ranar litini.
A can baya kanfanin ya taba bayyana cewa yayi tanajin kula da lafiyar kwakwalwa na musamman ga dukkan ma’aikatansa dake a wannan fanni.
Mun samo wannan labara ne daga shafin Reauters.
Facebook Forum