Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Ya Sake Barkew a Afirka Ta Tsakiya da Karuwar Asarar Rayuka


Dakarun Seleka
Dakarun Seleka

Rikicin kasar Afirka Ta Tsakiya sai kara dagulewa ya keyi sanadiyar sake barkewar fada da ya rutsa da rayuka da dama.

Rahotanni na cewa an sake samun barkewar munmunan tashin hankali a Afirka Ta Tsakiya kwana biyu a jere da mutuwar mutane kusan dari uku.

Joanna Manner jami'ar Amnesty a kasar ta shaidawa Muryar Amurka cewa 'yan bindiga dake da alaka da kawancen 'yan tawayen da suka hambare Shugaba Francois Bozize watan Maris suna kai mugun samame a babban birnin kasar Bangui.

Dakarun gwamnati da tsoffin mayakan Seleka suna bi gida-gida suna neman 'yan bindiga da aka sani makiyan Balaka ne suna yi masu kisa kiyashi barkatai.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ma'aikatanta sun kwashe akalla gawarwaki 281 kafin duhun dare ya tilasta masu dakatar da aikin ranar Juma'a.

Kasar Faransa ta kara yawan dakarunta a kasar bisa ga umurnin Hukumar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya ce lamarin da Afirka Ta Tsakiya ke ciki yana da muni.

A wani jawabi da ya yi ranar Juma'a ya ce rahotanni suna cewa akwai takunsaka tsakanin Musulmai da Kiristoci da kungiyoyin 'yan bindiga lamarin da yake da hatsarin gaske. Mayakan Seleka Muslmai ne yayin da masu kin jinin Balaka Kiristoci ne.

Faransa zata kara yawan dakarunta zuwa 1,200 kana kungiyar kasashen Afirka ta kara nata daga 2,500 zuwa 3,600.

Kasashen Turai sun yi alkawarin taimakawa abun da ya sa ranar Juma'a Biritania ta sanarda aika kayan yaki domin tallafawa kokarin Faransa.

Gwamnatin kasar ta Afirka Ta Tsakiya bata da wani iko domin ta kasa shawo kan 'yan tawaye wadanda suke cin karensu ba babbaka. Ana dorawa 'yan tawayen alhakin kashe-kashen mutane barkatai da yiwa mata fyade da yin fashi da makami da kwace motoci karfi da yaji.

Tun da kasar ta samu 'yanci daga Faransa a shekarar 1960 bata taba sani ko samun zaman lafiya ba.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG