Tashin hankalin ya barke yayinda kwamitin sulhu yake shirin kada kuri'a yau alhamis na tura karin dakarun Faransa zuwa kasar domin taimakwa wajen maido da doka da oda.
Majalisar Dinkin Duniya tace an kai harin ne ranar Litinin a wata al'umma dake tazarar kilomita casa'in dake arewa maso gabashin Bangui babban birnin kasar.
Amy Martin shugaban cibiyar ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya dake bangui yace akwai alamun cewa, mayakan Kirista da ake kira anti-balaka suna kai hare hare kan makiyaya Musulmi. A cikin sanarwar, tace, wannan na daga cikin tashe tashen hankali da aka fuskanta a baya bayan nan.
Faransa ta fara kokarin kara yawan dakarunta a jamhuriyar Afrika ta tsakiya da zuwa kimanin dubu daya.