Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fada Ya Barke A Gabon


Fada ya barke a Libreville, babban birnin Gabon, inda Shugaba Ali Bongo ya sake cin zabe ranar Laraba, zaben da aka ce na cike da magudi.

Rahotanni na nuna cewa masu zanga-zanga sun banka ma ginin Majalisar Tarayya wuta, su na ta cewa "Dole Ali ya tafi; Dole Ali ya tafi!"

Jaridar The Guardian ta ce da alamar jami'an tsaro sun bindige wasu mutane uku har lahira. Gwamnati dai ba ta tabbatar da wata mutuwa ba.

An dai girke 'yansanda a shataletalolin da ke fadin birnin.

Wakilin Muryar Amurka Adrissa Fall, wanda ya je hedikwatar hukumar zaben, ya ba da rahoton cewa wasu jami'an hukumar zaben sun yi murabus ranar Laraba.

Wanda ya ja da Bongo din, Jean Ping, ya ce kwamitin yakin nemar zabensa na da hujjojin da ke tabbatar da cewa an yi magudi a zaben kuma ya na shirin gabatar da su ga kotun kuntin tsarin mulki.

Sakamakon zaben, wanda ake gab da sanar da shi a hukumance, na nuna cewa Bongo ya ci da kashi 49.8% na kuri'un, shi kuma Ping ya samu kashi 48.2%.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG