Motar ta kara da katangar wani O'tel da ake kira SYL,wanda jami'an gwamnatin kasar suke yawan amfani dashi wajen gudanarda tarurruka.
"Wata mota cikin gudu ta yiwo ta kanmu. Muka yi harbi ta iska domin jan kunne. Motar bata tsaya ba, muka bude wuta kan motar, kamin matukinta ya tada nakiyoyi da aka dankarawa motar," ta bakin wani mai aikin tsaro a fadar shugaban kasar, wanda bai yarda a bayyana sunansa ba,a hira da yayi da Sashen Somalia na MA.
Shugaban motocin da suke jigilar maras a lafiya Dr. Abdulkadir Aden, yace kamfaninsa yayi jigilar gawarwaki 22, da mutane 30 wadanda suka jikkata. "shida daga cikin mutu mata ne," yace.
Jami'in 'Yansanda a birnin Mogadishu Manjo Mohammed Abdullahi ya gayawa kamfain dillancin labarai na Reuters cewa mutane 50 suka ji rauni sakamakon harin na jiya Talata.