Ethiopia tace tana da shaida mai yawa dake tabbatar da ana horar da yan tawayen, ana basu tallafin kudi a Masar, inji kakakin gwamnatin Ethiopia, Getachew Reda a hirarsa da manema labara a jiya Litinin.
Tun cikin makon jiya dai kasar Masar take ta musunta bada wani taimako ga ‘yan tawayen na Ethiopia.
Masar da Ethiopia sun dade suna samun rikici tsakaninsu a kan atun mallakar ruwan kogin Nilu, inda Masar ke cewa madatsar ruwan da Ethiopia ke ginawa a kogin zai rage yawan ruwan da Misra din ke samu.
Getachew yace dokar ta bacin watanni shidan da aka kafa zata baiwa gwamnati daman daukan kwararan matakai a kan kungiyar OLF da ta shirya tarukan zanga zanga a duk fadin jihar Oromia a makon da ya gabata.
Kungiyoyin kare hakkin Bil Adama da jami’an ‘yan adawa sunce mutane akalla 400 ne aka kashe a wannan zanga zanga ta kin jinin gwmanti a shekara da ta gabata.