Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

HUMAN RAIGHTS WATCH: Ta Soki Lamirin Dokar Yaki da Ta'addanci


Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi
Shugaban Masar Abdel-Fattah el-Sissi

Kungiyar kare hakkin bil adama ta (Human right Watch) ta soki lamirin sabuwar dokar nan mai nasaba da aikin ta’addanci wadda aka samar a kasar Masar.Kungiyar tace wannan dokar tafi karfin dokar aikata ayyukan taaddanci.

Kungityar tace wannan yana iya tura yan kasar ta Masar ga halin tujara ko kuma.

A ranar lahadi ne dai shugaban kasar Abdel Fattah El-sisi yasa wa dokar hannu, yin hakan ko ya biyo bayan kashe babban mai gabatar da kara ne na kasar dalilin da yasa shugaban yace za a samar da dokar da zata dauki mataki akamn duk wani ko wasu masu aikata ayyukan assha.

Wasu daga cikin hukuncin wannan dokar ko sun hada da hukuncin kissa ga dukkan wanda aka samu hannu cikin aikata ayyukan taaadanci ko kuma hukuncin daurin rai-da-rai ga dukkan wanda ya taimaka ko kuma ya tunzura jamaa domin aikata duk wani abu dake da nasaba da taaddanci.

Wannan dai yana nufin da wannan sabon dokar, kasar ta Masar ta dunfari hanyar tabbatar samar da dokar din-din-din, akan dokokin kasar.

Babban mukaddashin darektan kungiyar ta kare hakkin bil adama dake kula dakasashen arewa ta tsakiya da arewacin Africa Nadim Houry yace ba shakka gwamnati ta samar wa kanta babban makari da wannan dokokin domin ganin takakkabe masu sukan lamirin ta da zummar cewa tana yaki da yan taadda.

XS
SM
MD
LG