Shahararren mai jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, Okuneye Idris, wanda aka fi sani da Bobrisky yayi zargin cewar hukumar efcc, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta kama shi.
Hakan na zuwa ne bayan bayyanar wani faifan bidiyo a dandalin X dake nuna yadda aka sauke daga cikin wani jirgin saman kamfanin klm dake kan hanyarsa ta zuwa birnin Amsterdam a daren jiya Alhamis.
Bayan da aka sauke shi da karfin tsiya daga jirgin, shahararren dan daudun ya wallafa al’amarin a shafinsa na instagram domin sanar da masu bibiyarsa halin da ake ciki.
Bobrisky ya yi zargin cewar hukumar EFCC na da hannu a tsare shi da aka yi.
Inda ya wallafa cewar, “’yan Najeriya ku taimaka min, yanzun nan EFCC ta kama ni. Naji mummunan rauni.”
A ranar 20 ga watan Oktoba da ta gabata ne Hukumar shige da fice ta Najeriya ta ce ta kama Bobrisky a iyakar Seme da ta hada Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, hukumar ta ce ta kama Bobrisky ne yayin da yake “kokarin tserewa daga kasar.”
“Hukumar tana so ta sanar da jama’a cewa, Okuneye Idris, mutum ne da ake nema kan wani al’amari da ya shafi jama’a.
“Ana kan yi masa tambayoyi kuma za a mika shiga ga hukumar da ta dace.” Sanarwar dauke da sa hannun Kakakin hukumar, DCI Kenneth Udo ta ce.
Dandalin Mu Tattauna