Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ganduje Ya Bukaci 'Yan Najeriya Su Kara Hakuri Da Tinubu


Yana hawan kan karagar mulki a 2023, shugaban kasar ya sanar da bullo da wasu muhimman manufofi guda 2 na janye tallafin man fetur da kuma hade harkar musayar kudade a wuri guda.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, ya roki 'yan Najeriya su kara hakuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da sauye-sauyen da yake aiwatarwa wadanda suka haddasawa mutane da dama kuncin rayuwa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a sanarwar da babban sakataren yada labaransa, Edwin Olofu ya fitar yayin shagulgulan bikin kirsimeti na bana.

Yana hawan kan karagar mulki a 2023, shugaban kasar ya sanar da bullo da wasu muhimman manufofi guda 2 na janye tallafin man fetur da kuma hade harkar musayar kudade a wuri guda.

Nan da nan wadannan manufofi suka sabbaba hauhawar farashin da ba a taba ganin irinta ba a kasar, al'amarin da ya jefa dimbin 'yan Najeriya cikin halin ni 'ya su har ta kai ga da kyar suke iya ci da kansu.

Sai dai, a yayin da sakon tsohon gwamnan jihar Kanon ke kira da a kara hakuri, yace an fara tasirin sauye-sauyen gwamnatin Tinubun.

Ya kuma ba da tabbacin cewa kan nan da bikin kirsimetin badi, tattalin arzikin Najeriya zai kara daidaita, inda yace kokarin gwamnatin na samar da tsaro a fadin kasar ya fara haifar da da-mai ido kasancewar an samu matukar raguwar matsalolin 'yan bindiga da yin garkuwa da mutane.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG