Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa babu kuskure a harin jirgin saman da sojoji suka kaiwa gungun 'yan ta'addar Lakurawa a Sokoto a jiya Laraba.
Wani jirgin saman yaki ya jefa bama-bamai a kan wasu kauyuka 2 dake karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto, inda suka hallaka akalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama.
Gwamnatin jihar Sokoto ta yi ikirarin cewa mutane 10 da suka mutu a harin "kauyawa ne da basu ji ba basu gani ba."
Amma a ziyarar da ya kai jihar dake yankin arewa maso yamman kwana guda bayan afkuwar lamarin, babban hafsan tsaron ya zanta da manema labarai a barikin sojoji na Gingiya dake Sokoto, inda ya jaddada cewa wadanda aka hallaka din masu laifi ne. Sai dai yace za a kaddamar da bincike akan lamarin.
"Akwai mutanen da har yanzu suna baiwa irin wadannan mutane mafaka, kuma da zarar ka yi hakan ka ba da damar kai maka hari. Rokonmu a nan shine kada ku bari su zauna cikinku, kada ku basu kowane irin tallafi."
"Al'amarin da ya faru a jiya samame da muka kai. Mun bibiya domin tabbatar da mun kaucewa kurakurai yadda ya kamata. Idan ma akwai kurakuran da aka yi zamu bincika."
"Daga abin da muka gani, akwai masu laifi a wurin. Duk wanda keda alaka da su yana tare da su."
Dandalin Mu Tattauna