Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Na Farfadowa Daga Matsalar Katsewar Layin Internet Da Ya Haddasa Soke Tashin Jirage


Worldwide-Internet-Outage-Airlines
Worldwide-Internet-Outage-Airlines

Sannu a hankali layukan internet na kamfanonin jiragen sama sun fara dawowa yau Asabar bayan da kamfanonin sadarwa na duniya, da bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi suka fada cikin rudani sakamakon gagarumar katsewar layukan internet a cikin 'yan shekarun nan, don aikin sabunta matakin kariya.

Fasinjoji sun yi cunkoso a filayen tashi da saukar jiragen sama a ranar Juma'a don samun labarai yayin da aka soke tashin jirage da dama kana masu gudanar da gyare gyare sun kokarta don shawo kan lamari, bayan sabunta wani softiwaya da ake amfani da shi kan komfutar Microsoft da ya tarwatse a duk duniya.

Kamfanonin jiragen saman Amurka da dama da filayen jiragen sama a duk fadin nahiyar Asiya sun ce yanzu sun fara aiki, tare da dawo da ayyukan shiga a Hong Kong, Koriya ta Kudu da kuma Thailand, kana galibi ayyuka na komawa kamar yadda aka saba a Indiya, Indonesiya da filin jirgin sama na Changi na Singapore ya zuwa ranar yau Asabar.

Worldwide Internet Outage
Worldwide Internet Outage

Microsoft ya ce batun ya fara ne da karfe 7 na yamma agogon GMT a ranar Alhamis, wanda ya shafi masu amfani da komfutar Windows dake gudanar da manhajar tsaron yanar gizo ta Falcon da kamfanin CrowdStrike ya kera domin kariya daga masu kutse.

CrowdStrike ya ce ya dauki wani matakin gyara don magance matsalar kana shugaban kamfanin, George Kurtz, ya shaida wa tashar yada labarai ta Amurka CNBC cewa yana nemi afuwar kowace ma’aikata da kowace kungiya da kuma duk mutumin da lamarin ya shafa.

Tawagar shugaban Amurka Joe Biden na tattaunawa da kamfanin CrowdStrike da kuma wadanda matsalar ta shafa “kuma tana zaman jira ko za a bukaci wani taimako ta bayar,” a cewar wata sanarwar Fadar White House.

Worldwide Internet Outage
Worldwide Internet Outage

Rahotanni daga Netherlands da Birtaniya sun ce katsewar ta shafi ayyukan kiwon lafiya, lamarin da ke nufin ba za a iya sanin cikakken tasirin batun ba a yanzu.

Su ma kamfanonin yada labarai sun fuskanci matsalar, inda kafar yada labarai ta Sky News ta Birtaniya ta ce matsalar ta yanke shirin da ake yadawa da safiyar Juma'a, haka kuma ABC na Australia ya ba da rahoton manyan matsaloli.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG