A watan Agustan shekarar 2014 ne ‘yan sandan kasar Japan suka kai sumame gidan wani hamshakin maikudi mai suna Mitsutoki Shigeta, inda suka sami jarirai burjik tare da masu kula dasu.’yan sandan sunje wajen ne bisa labarin da suka samu na cewar yana safarar jarirai da yara kanana.
A yau litinin ne kuma kotun birnin Bangkok ta bashi damar karba da kuma rike yaran guda 13 da cewar shine ubansu amma daga iyaye mata daban daban, kuma ba’a same shi da laifin safarar jarirai ba.
Wannan abu ya ba mutane al’ajabi, inda suke ta tunanin dalilinsa na tara yara kamar haka, domin ya ce yana son yara akalla 10 zuwa 15 a kowacce shekara, asibitin da yake zuwa domin kai matan da ake dasawa kwai su Haifa masa yaran sun yi kokarin sanar da ‘yan sanda amman abin bai yiwu ba domin ‘yan sandan basu taba maida wa wasikar su martini ba.
An kai Shigeta, kotu sedai bai bayyana a gaban ta, lauyoyin da ke wakiltar sa sun bayyana cewa yayi hakan ne domin yana son iyali mai girma kuma yanada tsarin da yayi na musamman domin kula da wadannan yara, ciki akwai gida babba da wadansu kudade da ya ajiye.
Facebook Forum