Rananr Talata 20 ga watan Fabrairu shekarar 2018, tawagar mata ‘yan wasan zamiyar kankara, Moriam Seun Adigun da Akuoma Omega sun ci nasarar farko a wassanin Olympics na hunturu da ake yi a Pyeongchang a Korea ta Kudu lokacin da aka bayyana sakamakon wasan zamiyar kankara inda tawagar Nigeria, suka samu maki 52.21 duk da cewa sun kare a matsayi na 20.
Wannan nasara ta jawo murna da farin ciki a masaukin tawagar jami’an tarrayar Nigeria na wasan zamiya (BSFN) biyo bayan makin da ‘yan tawagar Nigeria suka samu a wasan zamiyar kankara ya wuce misali.
Darktan bayyana labarai na BSFN, Chisom Mbonu-Ezeoke ya ce ‘eh’’ wannan abin farin ciki ne kwarai yayinda da yake amsa tambayoyin kanfanin jaridar “Gaurdian’’ daga Korea ta Kudu ranar Talata bayan an kammala wassan.
Seun Adigun da Akuoma Omega sun bayyana cewa ba wai sun shiga wassan bane domin su lashe labar zinariya ko azurfa a wassan zamiyar kankara ba, amma akwai babban dalilin kasancewar su a Pyeongchang.
A matsayin su na tawagar farko ta wasan zamiya daga nahiyar Afrika, har abada sun zama misali na abinda ka iya faruwa idan mutum ya sa rai da mafarkin zai cimma buri a rayuwa. A cewar Eric Seals, mai bada rahoton wassanin na kafar labaran USA TODAY.
Facebook Forum