Dubban yan Nigeria a sassa dabam dabam na kasar sunyi zanga zangar nuna rashin amincewa cire tallafin mai, harma sunyi arangamomi da yan sanda da suka zama sanadin kashe mutane uku.
Shedun gani da ido sunce yan sanda sun harbe wani mai zanga zanga litinin din nan a birnin Ikko.
A wani wuri dabam kuma a birnin na Ikko, yan sandan kwantar da tarzoma sun lura a yayinda masu zanga zanga suka rufe ko kuma tare hanyoyi da konannun tayoyi a yayinda wasu ke furta la'anar manufofi shugaba Jonathan.
A birnin Kano dake arewacin kasar kuma, shedun gani da ido sunce mutane biyu aka harbe har lahira.. Kungiyar agaji ta Red Cross ta bada rahoton cewa akalla mutane goma sha hudu ne suka ji rauni, ciki harda mutun bakwai wadanda aka jiwa rauni a sakamakon harbe harbe da bindiga.
Jami'ai a Kano sun kafa dokar hana fita ta sa'o'i goma sha hudu, daga karfe shidda na yamma zuwa karfe takwas na safe. Hukumomi sun dauki wannan mataki ne a wani yunkurin maido da bin doka da oda.
Litinin dubban yan Nigeria suka fara yajin aiki, domin nuna rashin amincewarsu ga matakin da gwamnati ta dauka a makon jiya na cire tallafin mai.
Zanga zangar ko kuma yajin aikin tasa al'ummar sun tsaya ciki a biranen kasar ciki harda Abuja baban birnin taraiyar Nigeria.
Manyan kungiyoyin kwadagon Nigeria ne suka bukaci ayi zanga zangar domi matsawa gwamnatin lamba ta maido da tallafin,.