'Yan Najeriya sun ci gaba da bayyana fushinsu a yau talata, a yayin da dubbai suka yi cincirindo a fadin kasar domin su nuna rashin yardarsu da tashin gwauron zabin farashin mai a kasar, da kuma zarmiya da cin hanci na jami'an gwamnati.
A wannan rana ta biyu ta yajin aiki a fadin kasar, 'yan sanda a Lagos, cibiyar harkokin kasuwancin kasar, sun tsaya suka zuba ido a yayin da dubban mutane suka yi gangami su na sukar lamirin gwamnati, yayin da hayaki ke tashi sama daga tayoyin da suka kona a kan hanyoyi. matasa dake fusace sun tayar da wuta a kan hanyoyin domin hana shiga cikin wata unguwa ta masu hannu da shuni.
Wasu dubban kuma sun yi gangami a Abuja, babban birnin kasar. Masu zanga-zanga a Abuja sun yi yawan da sai da aka tura karin 'yan sanda zuwa wurin gangamin domin tabbatar da tsaro.
A birnin Benin dake kudancin kasar, wasu mutane dake fusace sun kai farmaki a kan wani Masallaci da wata makaranta. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce an kashe mutane biyar. Wani jami'in kungiyar yace watakila wadannan hare-hare na Benin su na da alaka da rashin jituwar da ake fama da ita a tsakanin Musulmi da Kirista a kasar.
An bayar da rahoton mutuwar mutane uku a ranar farko ta gangamin yaki da janye tallafin farashin man fetur a jiya litinin.
Manyan kungiyoyin kwadago na Najeriya sun lashi takobin yin yajin aiki har sai gwamnati ta maido da talafin farashin man fetur da ta janye a ranar 1 ga watan Janairu. Janye tallafin farashin ya sa kudin man fetur a kasar ya ninku cikin kwana guda.
haka kuma, farashin abinci da na sufuri yayi tashin gwauron zabi tun daga lokacin da aka janye tallafin farashin man.