Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara a Ma'aikatar Shari'a a Janhuriyar Nijar


A nan wata gobarar ce amman a Pakistan
A nan wata gobarar ce amman a Pakistan

Gobarar ta tashi ne da safiyar jiya Talata a ma’ikatar shari’a dake birnin Niamey

Gobarar ta tashi ne da safiyar jiya Talata a ma’ikatar shari’a dake birnin Niamey, gobarar, ta kuma yi babbar barna ga ginin ma’aikatar ta kuma kokkona muhimman takardun dake kunshe da bayanan ajiya da na tarihin kasa.

Jami’an hukumomin Jumhuriyar Nijer bayyana cewar daga cikin muhimman takardun bayanan da gobarar ta lalata, harda takardun shaida da kaset-kaset na bayanan da aka dauka ta wayar tarho dake da alaka da tattaunawar cin hanci da rashawar da Alkalan majistare keyi. An tattara wadannan bayanai ne da nufin gabatar dasu gaban shari’a.

‘Yan sanda sun ce abinda ba’a gano ba shine ko gobarar an tada ita ne da gangan, ko kuma afkuwar hatsari ne. Jumhuriyar Nijer kamar sauran kasashen Afirka, na fama da matsalar cin hanci da rashawa dake addabar jami’an Gwamnati.

Shugaba Muhammadu Issofou na Nijer yayi alkwarin bada fifikon daukan matakan kauada wannan matsala ta cin hanci da rashawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG