Duba Kan Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa A Najeriya Da Tare Motocin Dakon Abinci
A cikin shirin Taskar VOA na wannan makon, ‘yan Najeriya na ci gaba da kokawa da tsadar rayuwa, lamarin da ya sa NLC a kasar yin zanga-zangar neman hukumomi su dauki matakan saukake rayuwa. Mawuyacin hali da ake ciki a Najeriyar ya sa mutane a wasu wurare tare motocin abinci tare da yin warwaso.