Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tasirin Dokar Kare 'Yancin Kananan Yara a Najeriya-Kashi Na Uku-Agusta, 15, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Sashen farko na dokar kare kananan yara na cewa, wajibi ne a ba yaro fifiko a duk batutuwa ko yanayin da ya shafe shi. Ya ci gaba da bayyana cewa, wajibi ne iyaye ko mai kula da yaro su ba yaro kariyar da yake bukata. Sai dai kamar yadda bakin da shirin Domin iyali ya gayyata domin nazarin tasiri ko akasin haka na wannan dokar a Najiriya suka bayyana, har yanzu ana yiwa dokar mummunar fahimta.

A yau, shirin ya maida hankali kan abinda dokar ta kunsa da kuma yadda za a iya aiwatar da ita.

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tasirin Dokar Kare 'Yancin Kananan Yara a Najeriya-Kashi Na Uku
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:26 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG