Washington, DC —
A ci gaba da nazarin tasiri ko akasin haka na dokar kare hakkin kananan yara bayan sama da shekaru 20 da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa ta, batun da ya dauki hankalin babban taron kungiyar lauyoyi mata na kasa da jihar Kano ta karbi bakunci. Yau bakin da Shirin Domin Iyali ya gayyata sun bayyana abinda ya hana rungumar dokar.
Bakin da shirin ya gayyata sun hada daBarista Bilkisu Ibrahim Sulaiman shugabar kungiyar lauyoyi mata reshen jihar Kano, da Barrista Ibrahim Chedi tsohon ma’ajin kungiyar lauyoyi na kasa reshen jihar Kano, da kuma magidanci da ke wakiltar iyaye a wannan zaman Malam Aminu Muhammad Adam .
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna