Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Tasirin Dokar Kare 'Yancin Kananan Yara a Najeriya-Kashi Na Daya, Yuli 25, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A shekara ta 2003, Najeriya ta amince da dokar kare hakkin kananan yara don jihohi su amfani da ita bayan yi mata kwaskwarima yadda za tafi daidai da al’adu da kuma addinansu. Dokar kare hakkin yara ta 2003 ta fadada yancin dan adam da aka baiwa yan kasa a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ga yara. Duk da cewa an zartar da wannan doka a matakin tarayya, amma zata yi aiki ne kawai idan majalisun jihohi su ma sun rungume ta sun maida ita doka.

A yau shirin Domin Iyali zai fara nazarin tasirin wannan doka ko akasin haka shekaru sama da 20 bayan amincewa da ita a Najeriya, batun da aka gabatar aka kuma yi muhawara a kai a babban taron kungiyar lauyoyi mata na kasa da aka gudanar a birnin Kano.

Saurari cikakken shirin:

Domin Iyali: Kare Hakkin Kananan Yara Pt1
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:28 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG