Washington, DC —
Idan kuna tare damu, shiri Domin Iyali yana nazarin dokar da aka zartar a Najeriya shekaru goma da suka shige ta haramta cin zarafin mutane da ake kira (VAPP), da ya hada da cin zarafin mata, da cin zarafi a cikin gida. Ganin yadda dokar ta ke neman shiga kwandon mantuwa ya sa aka sake gabatar da ita gaban Majalisar tarrayyar Najeriya, lamarin da ya dauki hankalin wannnan shirin.
Shirin nya gayyaci mata ‘yan gwaggwarmaya Hajiya Hauwa Abubakar Funtua mai ba matar gwamnan jihar Katsina shawarwarwari, Jamila Sidi Ali Sirajo, da kuma Barrister Hassana Ayuba Mairiga Tula.
A yau, bakin sun bayyana abinda mata su ke so su gani an yi na hukumci kan wanda ya keta dokar.
Saurari cikakken shirin:
Dandalin Mu Tattauna