Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Dokar Haramta Cin Zarafin Bil'adama Kashi Na Daya- Nuwamba, 14, 2024


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A shekarar dubu da dari biyu da goma sha biyar, Najeriya ta zartar da dokar haramta cin zarafin mutane da ake kira (VAPP), ciki har da cin zarafin mata, cin zarafi a cikin gida, da kuma haramta bin al'adun gargajiya masu cutarwa. Dokar ta kuma bukaci bada kariya ta doka da ma'amala da tallafa wa wadanda abin ya shafa, da kuma hukunta masu laifi. Sai dai bayan kusan shekaru goma da kafa wannan doka a matsayin tarayya, har yanzu batun yana kasa yana dabo a galibin jihohin kasar.

Batun da Shirin Domin Iyali ya fara haska fitila a kai ke nan yau tare da Hajiya Hauwa Abubakar Funtua mai ba matar gwamnan jihar Katsina shawarwarwari, da ‘yar gwaggwarmaya Jamila Sidi Ali Sirajo, da kuma Barrister Hassana Ayuba Mairiga Tula.

Saurari cikakken shirihn:

DOMIN IYALI: Dokar Haramta Cin Zarafin Bil'adama Kashi Na Daya
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:13 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG