Kan matsalolin da ake fuskanta a duk fadin Najeriya ta rashin Man fetur da wutar lantarki dama ruwan sha, Dandali ya leka birnin Kano domin ganin yadda wannan matsala ke shafar matasan mu.
Wakiliyar Dandali Baraka Bashir dake jihar Kano ta zanta da wani matashi mai sayar da kayan masarufi, wanda ya koka kan rashin samun wadatar wutar lantarki wadda ke dakushe sana’ar sa, matashin mai suna Hassan Umar Gandun Albasa ya bayyana mana cewa kayan sanyi kamar su lemo da ruwan sanyi sune kayyayakin da suka fi tafiya a sana’ar sa, amma rashin samun wutar lantarki ta janyo musu rashin ciniki gaba ‘daya.
Hassan Umar ya koka kan yadda ba zasu iya amfani da injin ganareta ba don kuwa bazasu iya fitar da riba a cinikinsu. A dalilin haka ne suke sayo kankara wadda ita kanta daga jihar Kaduna ake kawo musu ita, ga kuma tsada.
Wanan matashi dai yace rashin wuta ya sa kastomomin sa sun ragu, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta duba irin wahalar da masu kananan sana’a’oi ke sha tayi musu maganin ta.