WASHINGTON, DC —
Kusan shekara daya ke nan da kungiyar dattawan arewa ko AEF a takaice ta kafa wani kwamiti wanda yawancin wadanda ke ciki lauyoyi ne domin tara bayanai kan yadda dakarun tsaron Najeriya musamman sojoji suka gudanar da ayyukansu a arewa maso gabashin kasar.
Wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda ta zanta da shugaban kungiyar dattawan arewa Farfasa Ango Abdullahi yayin da ya yi taro da kwamitin binciken da kungiyar ta kafa. Musamman kungiyar ta bukaci kwamitin ya duba irin canje-canjen da ake so a kawo a tsarin mulkin Najeriya a matsayin aikin farko. Daga baya sabili da abubuwan da suke faruwa a arewa maso gabas, musamman yakar kungiyar Boko Haram, kungiyar dattawan ta ga ana ta barna da rayukan mutane sai ta umurci kwamitin ya tara bayanai.
Kungiyar ta lura cewa akwai alamu da suka nuna sojoji da 'yansanda basa bin ka'ida wurin gudanar da ayyukansu domin neman zaman lafiya wanda suke ikirarin tabbatarwa. Farfasa Ango Abdullahi ya ce rahotanni daga cikin gida da waje sun nuna abubuwan da dakarun tsaron Najeriya keyi suna yin barna. Sabili da haka dattawan suka sa ido su tabbatar da zargin da aka yi kuma duk alamu sun nuna an yi hakan. Abun da ya rage kawai a tabbatar da shaida domin idan za'a kai magana gaban mai shari'a dole sai an tabbatar da shaida da zata gamsheshi cewa lalle an aikata barna.
Cikin watannin da suka wuce kungiyar dattawan ta shiga tattaro bayanai da zata yi anfani da su a kotun kasa da kasa ta tabbatar cewa an yi barna da sunan kawar da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.
Kwamitin ya bayar da labarin abun da ya yi tun lokacin da aka kafashi har zuwa lokacin taron. Kungiyar dattawan ta duba abubuwan da take ragin sojoji da yi kuma zata bi hanyar samunsu. Cikin 'yan kwanaki masu zuwa dattawan zasu je jihar Borno su gana da dattawan jihar domin su samu abun da kungiyar bata da shi ita ma kungiyar ta baiwa dattawan Borno abubuwan da basu da shi domin bangarorin biyu su karu da juna. Bayan ganawar zasu kai matsayin da zasu iya shigar da kararsu a kotun kasa da kasa.
Ga karin bayani.