Duk da cewa mutane sun cika makil a gidajen ministocin da Buhari ya nada, ministocin na kokarin bayyana masu cewa canji zasu kawo.
Sabon ministan zirga zirgan jiragen sama Hadi Sirika yace babu dalilin cin hanci da rashawa. Ba zata yiwu ba yana minista ya dauki kwangila bya ba kansa ko ya ba dansa ko matarsa.
Duk wanda zai ba kwangila dole sai ya bi kai'dodin da aka tsara. Duk 'yan Najeriya daidai suke. Duk wanda ya zo neman kwangila ya bi ka'ida. Idan an bi ka'ida babu yadda cin hanci zai biyo. Idan mutum ya bi ka'ida kuma bai samu ba sai ya hakura. Yace cikin mutanen da shugaba Buhari ya zakulo babu wanda yake da halin cin hanci da rashawa.
Akan ko sabon ministan zai shawo kan shugaba Buhari ya dawoda kamfanin jirage wato Nigerian Airways sai yace za'a yi shiri wanda zai samarda kamfanin da ya fi wancan tsohon dacewa da tsari.
A bayan fage tsohon shugaban matasan kiristocin Najeriya Pastor Simon Donli yace nan gaba yakamata a duba bangaren matasa. Yace an ce matasa su ne shugabannin gobe idan kuma haka ne kamata ya yi a soma kawosu kusa saboda su ma su koya. An nada ministoci 36 amma babu matashi ko daya. Ba'a kyautawa matasa ba.
Ga karin bayani.