Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kaddamar Da Shugabannin INEC


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Yau shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da shugabannin hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu inda aka biki a fadar gwamnati da ke Abuja.

Yayin gudanar da wannan biki, shugaba Buhari ya yi jawabi kan tarihin zabe a Najeriya da irin alkawuran da gwamnatinsa ta yiwa ‘yan Najeriya kafin zabe tare da la’akkari da cewa za a baiwa hukumar cikakken iko.

“Mun yiwa ‘yan Najeriya alkawari za mu baiwa hukumar zabe mai zaman kanta cikakken iko domin gudanar da ayyukanta ba tare da sa baki ko tsangwama ba, kuma a shirye na ke na ci gaba da cika wannan alkawari.” In ji Buhari.

Bayan kammala taron, sabon shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya jinjina yadda shugaban ya ce zai tsame hannunsa daga kan hukumar.

“Shugaban na Najeriya ya bamu tabbacin cewa ba zai yi mana katsalanda ba, kuma idan shugaban kasa ya ce ba zai yi katsalandan ba wa za mu ji tsoro. Saboda haka babu gudu ba ja da baya ba mu da abokan gaba da ba mu da abokai.” In Ji Farfesa Yakubu.

Ya kuma kara da cewa duk abubuwan da suka sa aka yi zabe mai inganci a baya daga nan zai dora domin a tabbatar da dorewar dimokradiyya.

Yanzu dai an sa ido a ga irin kamin ludayin sabon shugaban hukumar ta INEC a zabukan da za a yi a jihohin Kogi da kuma Bayelsa.

Ga cikakken rahoton da wakilin Muryar Amurka Umar Musa Faruk ya aiko mana:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG