Bayan da ‘yan kungiyar kishin muradun kabilar Yarbawa ta OPC shiyyar jihar Ogun ta kashe wata mata a yayin wani sintirinsu na kare bututun mai, an sake shiga takaddama kan halaccin kungiyoyin sa kai na tsaro, wadanda tun bay au ba ake ta tababa kan alfanun barinsu.
Wakilinmu na jihar Lagos Babangida Jibrin, ya ce tuni ma aka shiga kiraye kirayen gwamnati ta kwace wannan damar da aka ba su, a bai wa ‘yan kungiyar tsaron farin kaya ta Civil Defense, kamar yadda doka ta tanada. Wani da abin ya faru a idonsa ya shaida ma gidan talabijin a Lagos cewa lallai sai a kwace wannan iko da aka bai wa OPC a mika ma ‘yan sanda kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Kan wannan kiraye kirayen da ake ma gwamnati, Babangida Jibrin ya tuntubi wani lauya mai zaman kansa mai suna barrister Abubakar Sarkin Daji, wanda ya ce tun da farko ma dai bai wa irin wadannan kungiyoyin sa kai irin su OPC ikon tsaro da gwamnati ta ba su ya saba ma dokar kasa kuma nuna gazawa ne da kuma kaskantar da kai. Y ace akai rukunonin tsaro dabandaban a kasar wadanda ya kamata a sa su su kare duk wata kadara ta gwamnati amma ba kungiyoyi irin OPC ba. Ya ce irin wadannan kungiyoyin tamkar ‘yan ta’adda ne kawai.
Y ace abin da gwamnati mai baring ado ta yin a bai wa irin wadannan kungiyoyin iko sam bai dace ba, don haka ya kamata gwamnati mai ci ta gaggauta hana irin wadannan kungiyoyin amfani da ikon da bas u da shi a kundin tsarin mulkin kasa. Ya yi nuni da kungiyoyin tsagerun Naija Delta, wadanda aka bas u ikon tsaron man kasa, wanda y ace sam hakan bai dace ba kuma daure ma karya da kuma miyagu gindi ne kawai. Sai ya ce to idan kasa ta samu matsala yaya za a yi da irin wadannan makaman da ke hannu ‘yan Naija Delta da sauransu?