Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban makarantar sakandare ta Kano sun rasa rayukansu a hadarin mota


Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje

Dalibai goma sha biyu jihar Kano ta tura zuwa Legas domin gasar ilimin fasaha wanda suka kammala lami lafiya amma akan hanyarsu ta dawowa suka yi hadari tsakanin Legas da Ibadan

Tara daga cikin daliban Allah ya yiwa rasuwa a hadarin yayin da sauran aka kaisu asibiti saboda a yi masu jinyar raunukan da suka samu.

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya gana da iyayen yaran da 'yanuwansu a gidan gwamnati gabanin kawo gawarwakin daliban da maraicen jiya.

'Yanuwan wadanda suka rasa rayukansu sun fadi albarkacin bakinsu. Wasu sun yi addu'a Allah ya gafarta masu domin sun amince da duk abun da Allah ya yi.

Wata cikin kuka da juyayi tace mahaifin daya daga cikin yaran da suka rasu baya iya tashi saboda jikinsa sai gashi kuma ya rasa dansa.

Muhammad Dalhatu Adam da dansa yake cikin matattun yace Ubangiji ya fi kowa sani. Lokacin da suka samu labari abu ne mai sosa zuciya amma kuma babu abun da zasu ce saidai su yadda da abun da Allah ya yi.

Malam Ibrahim Khalil malamin addinin musulunci yace kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya fada duk wanda ya rasu a wajen bakunta ya yi mutuwar shahada. Saboda haka yaran da suka mutu a wajen bakunta sun yi mutuwar shahada. Irin wadannan abubuwa sukan faru domin Ubangiji ya nuna mana ikonsa.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG