Shaidun gani da ido sun ce fada ya barke a muhimmin birni na Abidjan, tsakanin sojoji da gyauron mayakan da ke biyayya ga hambararren shugaba Laurent Gbagbo. Mazauna wurin sun ce fadan na jiya Talata ya fi tsanani ne a Yopougon da ke gefen birnin Abidjan. Wani jami’in kungiyar agaji ta Red Cross ta gaya wa Associated Press cewa ma’aikatan kungiyar sun gano gawarwaki a kalla 40. Wannan yamutsin ya dada nuna irin kalubalar da kasar ke fuskanta a kokarinta na maido da yanayin tsaro, tun bayan mummunar jayayyar shugabanci tsakanin shugaba Alassane Ouatara, wanda ya ci zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan Nuwamba, da kuma Mr. Gbagbo wanda ya ki ya mika ragamar iko. Mr. Ouatara ya amshi ragamar iko a watan jiya bayan da magoya bayansa, tare da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da dakarun Faransa, suka kama Mr, Gbagbo a gidansa. Takaddamar shugabanci tsakanin mutanen biyu, ta salwantar da rayukan daruruwan fararen hula, ta kuma raba kimanin mutane miliyan guda da muhallansu.
Shaidun gani da ido sun ce fada ya barke a muhimmin birni na Abidjan, tsakanin sojoji da gyauron mayakan da ke biyayya ga hambararren shugaba Laurent Gbagbo