Jiya Talata gwamnatin Pakistan ta yi kakkausar suka game harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar Shugaban al-Ka’ida Usama bin Laden, tana mai gargadin cewa karfa wasu kasashe su dauka cewa suna da ikon shiga da fita cikin kasar ta Pakistan. Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta nuna matukar damuwarta da kin amincewa da yadda Amurka ta gudanar da wannan harka ta soji ba tare da sanar da ita ko samin izininta ba.Ta ce hukumar leken asirin Pakistan (ISI) ta sha yin musayar bayanai da hukumar leken asirin Amurka game da wannan gida da ke birnin Abbottabad da ke arewacin kasar. Ma’aikatar ta kara da cewa hukumar ta CIA da sauran hukumomin leken asirin da suke hulda da su, sun amfana da irin bayanan sirrin da hukumar ta ISI ke ba su.To amma gwamnatin Asif Ali Zardari na fama da karin matsin lamba cewa ta bayyana yadda aka yi dan ta’addan da aka fi nema a duniya ya boye a wani katafaren bene a garin da ke cike da sojoji, ciki har da wata jami’ar sojoji, kuma kusa da babban birnin kasar. A wata kasidar da aka buga a jaridar The Washington Post a jiya Talata, Mr. Zardari ya yi watsi da zargin cewa hukumomin Pakistan sun bayar da kariya ga bin Laden.
Jiya Talata gwamnatin Pakistan ta yi kakkausar suka game harin da Amurka ta kai wanda ya yi sanadin mutuwar Shugaban al-Ka’ida Usama bin Laden