Wannan shirin bada kariyar na wucin gadi dake kare dubban ‘yan kasar dake a tsakiyar nahiyar Amurka daga mayar da su kasarsu, bayan da suka samun kariya tun faruwar mummunar girgizar kasa da ta ragargaza kasarsu a shekarar 2001, zai kare ne ranar 9 ga watan Satumbar shekarar 2019.
A ranar ne, duk ‘yan kasar ta El Salvador dake zaune suna aiki a Amurka tun kusan shekaru 20 da suka gabata zasu koma karkashin tsohon tsarin farko da aka dora su akai, muddin har yanzu suna karkashin tsarin. Haka kuma suna da zabin neman wasu takardun iznin zaman kasa a bisa hujjar aiki ko kuma alakar iyali.
Wannan hukunci da aka yanke ba shakka zai jefa wasu ‘yan kasar El-Salvador da basu da takardun zaman kasa fuskantar mayar da su kasarsu ba tare da bata lokaci ba.
Facebook Forum