Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Netanyahu Ya Ce Majalisar Dinkin Duniya Ta Janye Agajin Da Take Ba Falasdinawa


Firayim Minista Benjamin Netanyahu
Firayim Minista Benjamin Netanyahu

Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya shaidawa majalisarsa a ranar lahadi cewa bangaren majalisar dinkin duniya da ke taimakawa ’yan gudun hijirar Falasdinu na kara matsalar ne kuma ya kamata a rufe shi.

Netanyahu ya koka akan yadda hukumar bada agajin majalisar dinkin duniya (UNRWA) ta maida hankali kawai kan yan gudun hijirar falasdinu, kuma ya kamata a maida akalar kudaden su kan hukumar da take kula da dukkan ‘yan gudun hijra a fadin dunya.

Hukumar tace akwai yan gudun hijira miliyan 5 da suka chanchanta a basu kulawa kankashin ta.
Akwai palasdinawa da suka bar gidajen su a lokacin da ake yakin kaddamar da Israila a shekarar1948.

A yau palasdinawa fiye da miliyan 1.5 na zaune a sansanonin gudun hijira dake Jordan Lebanon, Syria, West bank da kima Gaza.

Mai Magana da yawun UNRWA Chris Gunnes, yace hukumar zata ci gaba da aiki har sai an samarwa yan gudun hijirar masalaha mai dorewa.

Gunness a wani bayani da ya bayar tace abin da yake ta’asassa matsalar ‘yan gudun hijirar shine kasawar da bangarorin sukayi na fuskantar matsalar.

Lamarin nan na bukatar a gyara daga wadanta abin ya shafa ta hanyar gudanar da shawarwarin lumana a bisa tsarin kuduri da dokar kasa da kasa na majalisar dinkin duniya, kuma yana bukatar saka hannun sauran kasashen duniya .

Duk wani kokari na ganin an kawo zaman lafiya tsakanin Israila da Falasdinu ya gagara kuma abin ya kara tabarbarewa a lokacin da shugaban Amurka Donald Trump yayi kokarin maida Qudus babban birnin Israila a watan da ya gabata.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG