Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Siriya Na Fuskantar Matsalar Jin 'Kai Mai Tsanani


Shugaban Sashin Agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi jiya Litini cewa Siriya na fuskantar matsalar jin kai mafi tsanani a wannan lokaci; kuma lokaci na kurewa kan bukatar ceto dubban farar hula masu bukatar abinci, da ruwa da magunguna.

"A birnin Aleppo, akwai yiwuwar mu ga mummunar matsalar jinkai wadda ba a taba gani ba a tsawon shekaru biyar da aka yi ana zubar da jini da aikin rashin imani a yakin na Siriya," a cewar Stephen O'Brien ga Kwamitin Sulhun MDD a yawabinsa na wata-wata kan wannan batu.

"Kamar yadda na ce a baya, ya kamata in yi duk abin da na ke iyawa in jaddada bukatar tsagaita wuta ta tsawon sa'o'i 48 tare da yaddar bangarorin biyu, saboda a samu sukunin kai kayan agaji a dukkan sassan Aleppo."

Tun watan jiya MDD ta ke ta kiraye-kirayen a rinka tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 48 a fadan da ake yi a Aleppo, saboda a samar da kayan agaji ga marasa lafiya da kuma wadanda su ka samu raunuka.

O'Brien ya ce a shirye MDD ta ke ta tura motocin daukar kaya da 70 makare da kayan agaji zuwa gabashin Aleppo da zarar ta samu cikakken tabbacin tsaro.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG