WASHINGTON DC - Kisan gillar da aka yiwa sojojin a makon daya gabata a yankin Naija Delta a wani al'amarin daya jefa rundunar sojin Najeriya cikin garari ya janyo cece kuce a fadin Najeriya.
An kone kauyen Okuama dake karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta inda al'amarin ya faru, sakamakon kisan gillar, abinda ya kara fargabar harin ramuwar gayya daga sojojin.
Saidai Babban Kwamandan Rundunar Sojin Najeriya ta 6 ta hadin gwiwa dake aikin wanzar da zaman lafiya a yankin kudu maso kudancin kasar nan me taken: "Operation Delta Safe" a turance, Manjo Janar Jamal Abdussalam ya baiwa shugabannin Naija Delta tabbacin cewar dakarun zasu nuna kwarewa wajen kamo wadanda keda hannu a kisan gillar.
Sanarwar da rundunar sojin Najeriya ta fitar a jiya alhamis, ta ruwaito Manjo Janar Abdussalam na bada tabbacin cewar dakarun dake aikin farauto masu kisan gillar zasu yi aiki da takwarorinsu dake kauyen Okuama domin sanin makama da kwarewa a aikin da zasu gudanar a yankin.
Kwamandan ya bayyana hakan ne a yau juma'a 21 ga watan Maris din da muke ciki sa'ilin da shugaban hukumar NDDC ta raya yankin Naija Delta, Dr. Samuel Ogbuku ya kai masa ziyarar ta'aziya a shelkwatar rundunar hadin gwiwar dake barikin sojoji ta birnin Fatakwal.
Da yake yabawa shugaban hukumar ta nddc da tawagarsa game da ziyarar ta'aziyar, Manjo Janar Abdussalam yace aikin da Babban Hafsan Sojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya dorawa rundunar shine na kwato makaman da masu kisan gillar suka sace da kuma tabbatar da an kama dukkanin masu hannu a aika-aikar.
Ya kara da cewar, dakarun zasu cigaba da aikinsu a yankin har sai sun cimma burinsu.
Dandalin Mu Tattauna