Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Abdulsalami Yayi Allah Wadai Da Kisan Gillar Sojoji 17 A Delta


Janar Abdussalam Abubakar
Janar Abdussalam Abubakar

Tsohon Shugaban Mulkin Soja a Najeriya, Janar Abdussalam Abubakar yayi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa sojojin Najeriya 17 a jihar Delta dake Kudancin kasar.

Janar Abdussalam Abubakar wanda shine Shugaban cibiyar wanzar da zaman lafiya a Najeriya yace lamarin kisan sojojin abin takaici ne bisa la’akari da yadda jami’an tsaron Najeriya ke iya kokari wajan tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Rundunar sojojin Najeriya ta "Operation Hadin Kai" a bakin aiki (Facebook/Nigerian Army)
Rundunar sojojin Najeriya ta "Operation Hadin Kai" a bakin aiki (Facebook/Nigerian Army)

A yayin zantawar shi da manema labarai albarkacin wannan wata na Ramadan¸ Janar Abdussalam Abubakar yace a gaskiyar lamari ‘yan Najeriya na cikin wani hali na tsadar rayuwa a saboda haka ya bukaci masu hali da su taimakawa na kasa.

Ko da yake bai yi wani dogon sharhi ba game da kin bude bodar Najeriya da Nijar, ya nuna bukatar ganin an yi abin da zai taimakawa talakawan kasashen biyu.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG