Rahotanni daga Mexico na cewa, dan takarar shugaban kasa mai ra’ayin sauyi, wanda ya sha alwashin zai “gyarawa shugaba Donald Trump zama,” na gab da lashe zaben shugaban kasar da aka yi.
Kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka kada gabanin zaben na jiya Lahadi, ya nuna Andres Manuel Lopez Obrador, wanda aka fi sani da AMLO a takaice, shi zai yi nasara a zaben.
An yi ta ta-da jijiyar wuya tsakanin Mexico da Amurka, musamman dangane da yadda gwamnatin Trump ke aiwatar da tsarin “ba-sani-ba-sabo”, wanda ya kai ga raba ‘ya’ya da iyayensu, wadanda mafi aksarinsu ‘yan kasar ta Mexico ne akan iyakar kasar da Amurka.
Zaben shugaban kasar na Mexico ya wakana ne hade da na ‘yan majalisar dokoki da kuma gwamnoni tara.
Wannan zabe shi ne mafi girma a tarihin zamanin baya-bayan nan, kuma shi ne wanda aka fi samun tashin hankali, inda aka kashe sama da ‘yan siyasa 100 gabanin zaben na jiya lahadi.
Facebook Forum