A yau asabar din nan tashin bama bamai suka girgiza birnin Tripoli a yayinda kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta kai hare haren ba saban ba da rana. Kungiyar NATO tace ta auna wata motar adana na tafi da gidanka a wani gida da a wasu lokutan shugaba Gaddafi yana zama a cikinsa. Kamfanin dilanci labarun Faransa ya bada labarin cewa ana gani hayaki na tashi daga inda bam din ya fashe. Tunda farko a yau asabar hare haren da NATO ta kai sun haskaka sararin samaniyar birnin Tripoli. A halin da ake ciki kuma, kasar Rasha wadda daddiyar kawar Libya ce, tayi tayin shiga tsakani a kula yarjejeniyar da zata sa shugaba Gaddafi ya sauka daga ragamar mulki. Shugaban Rasha yace shugaba Gaddafi zai sauka daga kan ragamar mulki. Shugaban na Rasha yayi wannan furucin ne a jiya juma’a a karshen taron kolin kungiyar kasashe masu arzikin masana’antu a kasar Faransa inda kuma ya bada sanarwar cewa zai tura wani wakilinsa zuwa birnin Benghazi, babar tungar yan tawaye. Tunda farko a jiya juma’a sojojin dake biyaya ga shugaba Gaddafi sun sabunta yunkurin sake kwato birnin Misrata wanda ke hanun yan tawaye. Bangarorin biyu sun fafata a unguwani da dama na birnin.
A yau asabar din nan tashin bama bamai suka girgiza birnin Tripoli a yayinda kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta kai hare haren ba saban ba da rana. Kungiyar NATO tace ta auna wata motar adana na tafi da gidanka a wani gida da a wasu lokutan shugaba Gaddafi yana zama a cikinsa.