Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Gudun Hijira daga Sudan ta Kudu Dubu 920 Ne Suka Samu Mafaka a Uganda


Wasu 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu
Wasu 'yan gudun hijira daga Sudan ta Kudu

Kasar Uganda, wacce aka sani saboda karfin gwuiwar da take bayarwa gameda lamarin ‘yan gudun hijira, yanzu haka tana daukan bakuncin mutane fiyeda milyan 2 da dubu 200 masu neman mafaka, wadanda kuma suka hada da ‘yan kasar Sudan kamar dubu 920.

To amma yanzu da alama Uganda din ta soma jin jiki daga wannan nauyin, ta soma neman agajin kasashen duniya.

Frayim-Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda, yace a cikin watani shidda da suka gabata, kusan kullum sai Uganda ta karbi bakunci mutane kamar 2,000 dake gudun hijira, abinda yace yana dada nauyi akan hukumomin kasar a kokarinsu na samarda kayan masarufi kamar ruwan sha, kiyon lafiya da ilimi.

Dangane da hakan ne aka shirya cewa a watan gobe, shugaban Uganda din, Yoweri Museveni, da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, Antonio Guterres da kuma shugabannin hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD din zasu jagoranci wani taron bude asusun neman tallafin Dala milyan dubu 2 a kowace shekara, har tsawon shekaru hudu, don gudanar da aikin kula da ‘yan gudun hijiran.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG