WASHINGTON, DC —
A yayin da ake bayyana tababar yiwuwar gudanar da babban taron jam'iyyar CPC gobe asabar, rassan jam'iyyar a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun gudanar da taro a Bauchi, domin tsara yadda wannan jam'iyya zata hade da sauran jam'iyyun adawa wajen kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki a zaben 2015.
Taron ya kaddamar da wakilan jam'iyyar wadanda uwar jam'iyya ta kasa ta nada domin jagorancin tsare-tsaren hadewar, da kuma kimtsa ita kanta jam'iyyar ta CPC domin hadewa da masu adawa su kioma sabuwar jam'iyya ta APC.
Daya daga cikin jigogin jam'iyyar a Jihar Bauchi, Injiniya Sadiq Mahmud, yayi karin bayanin wannan taron nasu ma wakilinmu Abdulwahab Muhammad: