A hirar da yayi da Muryar Amurka, Janar Buhari ya ce bai kamata gwamnati ta zauna kawai ta sanya idanu yayin da ake ci gaba da yin abubuwan da suke kokarin rushe kasar ba.
Muhammadu Buhari yace shirin ahuwar da ake magana a kai a Najeriya zai yi aiki, amma sai idan an san su wanene a zahiri shugabannin kungiyar Boko Haram da ake son tattaunawa da su, kamar yadda aka yi na 'yan yankin Niger Delta.
Sannan kuma, ya sake nanata furucin da yayi tun farko cewa yanzu a Najeriya, akwai kungiyoyi uku dake kai hare-hare da sunan Boko Haram: watau kungiyar jama'ayu Ahlus Sunnati Lidda'awati Wal Jihad ta zahiri, da 'yan fashi dake fakewa da sunan wannan kungiya su na sata, da kuma 'yan ta'addar gwamnatin tarayya dake kashe mutane.