Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Yadda Azumin Bana Ya Banbanta Da Na Bara A Amurka


Ifaar food distribution
Ifaar food distribution

A kowacce shekara a watan azumin Ramadan, yawancin masallatai a Amurka su na raba abinci ga jama'a a lokacin buda baki. A wannan karon, an raba abincin ne daga cikin mota.

A wannan shekarar, miliyoyin Amurkawa sun yi allurar rigakafin coronavirus, kuma masallatai sun gudanar da ibadu.

Muryar Amurka ta tattauna da limamin masallacin Washington Islamic Center, inda muka fara da tambayar shi yadda azumin bana ya bambanta da na bara.

“Game da annobar Covid-19, mun san wannan ya shafe dukkanmu ne, da farko mun ga rashin zuwan mutane masallaci, mutane da yawa sun daina zuwa sallah na yau da kullum akai-akai, kuma idan har sun zo, dan kalilan ne." Imam Faisal Khan ya ce.

Ya kara da cewa, "muna da jami’ai da suke tabbatar an saka takunkumin rufe baki da hanci. Suna aiwatar da dokokin sosai, saboda ba kawai za a rufe baki da hanci ba ne, amma a tabbatar da kowa ya kawo dardumar sallarsa da kuma bin ka'idojin bada da tazara da juna a masalaci."

Iftaar food distribution
Iftaar food distribution

Mun kuma tuntubi wasu daga cikin musulmai dake zuwa ibada wannan wuri, yadda suka ji a bana, ganin cewa ba su samu yin ibada a wannan wuri ba a bara.

“A wannan watan na Ramadana, duk da cewa a mota muke karbar abinci, kuma hakan ya sa mun yi nesa da juna amma masu bada abincin suna samun albarkar saboda ciyar da mutane da suka yi.” Zahrah Ghanim ta ce.

Karin bayani akan: Covid-19, coronavirus, Allah, Ramadan, Muryar Amurka, da Amurka.

A tashi mahangar, Jamal Abdulkarim, na ganin annobar ta koya mana hulda da juna ta yanar gizo.

Shi kuwa Olatunde Musa Abubakar yana ganin akwai babban bambanci tsakanin azumin bana da na bara, sobada mutane suna farin ciki sosai, ko don ganin juna ma wata ni'ima ce daga Allah.

Shi ma Imam Musa Abubakar, bahaushe kuma dan asalin Ghana, ya ce Ibada a Masallaci a wannan shekaran, sai da aka hada da yin taka tsan-tsan.

Duk da cewa an samu ci gaba a bana, mutane da dama na fatan za a iya shawo kan cutar gaba daya kafin azumin Ramadan na badi, domin Masallatai su koma harkokinsu kamar a baya, mutane kuma su samu yin ibada kamar yadda suke so a Masallatai.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

XS
SM
MD
LG